Najeriya na ‘daya daga cikin kasashen da ake gallazawa manema labarai, ‘yan jarida da a kowacce rana suke fadi tashin zakulo rahotannin ba daidai ba, tare da manufar kawo sauyi domin ci gaban al’umma, suna fuskantar nau’o’i daban-daban na cin zarafi a Najeriya.
Cin zarafin ‘yan Jarida shine makasudin wani gangami na bai ‘daya da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya ta shirya a duk fadin kasar, domin nuna turjiya da rashin amincewa da cin zarafin da ake yiwa ‘yan jarida, musamman ta bangaren jami’an tsaro da ‘yan siyasa.
Mataimakin shugaban ‘yan jarida Shehu Usman, wanda shine ya jagoranci zanga-zangar da aka gudanar a Sokoto, ya ce wajen samo labaran siyasa shine na biyu mafi hatsari bayan wajen yaki.
Rahotan wani kwamitin kare ‘yancin ‘yan jarida ya saka Najeriya a zaman ta 11 daga cikin jerin kasashe 12 da aka fi gallazawa ‘yan jarida a duniya.
Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk.
Facebook Forum