Hukumar Gidan Yarin Najeriya Ta Samu Shaidar Karramawa Da Kyautar Kudi

profit prison

Hukumar gidajen yarin Najeriya ta samu kyautar karramawa ta hukumar asusun ilimi na Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, kan ba da dama ga fursunoni su ci gaba da karatu da hakan kan kai su har matakin digiri.

Daraktan labaru na budaddiyar jami’ar Najeriya “NOUN” Ibrahim Sheme ya ce jami’ar ce ke aikin karantar da fursunonin inda har a bara ma ta yaye dalibai a gidan yarin KIRIKIRI da ke Lagos.

Ibrahim Sheme ya ce za a gudanar da taron mika kyautar a birnin Paris a farkon watan nan na Satumba mai shigowa daidai ranar yaki da jahilci ta duniya.

Bayan nan shugaban hukumar gidan yari na Najeriya da shugaban jami’ar NOUN, sun samu gaiyatar zuwa Sin don ziyartar garin wani shaharerren mai raya ilimi na kasar CONSPICIUS da a ka radawa wannan kyauta sunan sa.

Kyautar dai baya ga allon lambar yabo ta hada da kudi dala dubu ashirin.

Ga karin bayani a zantawa daga Ibrahim Sheme a wannan zantawa.