Za'a Iya Tabawa, A ji, A Gani Duk A Fasahar Haske Mai Kwakwalwa A Duniya

Wata fasaha da aka kirkiro wajen amfani da haske, jin magana, daga wata duniya zuwa wata. Fasahar na amfani da kwakwalwar mutun wajen bayyana ma mutun wata duniya da abubuwa dake gudana a duniyar.

Cigaban kimiyyar ya samar da karin hanyar da mutun zai gani ya kuma ji, kana ya taba wasu abubuwa da ya gani a wata nahiyar, duk ta amfani da tsarin da aka yi ma lakani da ‘Virtual Reality’

Masana sun bayyana tsarin kimiyyar hasken dake bayyana a kwakwalwar bil’adama a matsayin cigaban kimiyya, domin kuwa a duk lokacin da mutun yake amfani da tsarin, zai iya ganin wata kasa da kuma jin maganganu daga kasar, kuma zai iya taba abubuwa da suka bayyana a hasken na’urar sa.

Kamfanin kasar Faransa, ‘Go Touch VR’ wanda ya kirkiri fasahar ‘VRtouch’ da mutun zai makala a ‘yan-yatsunsa inda a duk lokacin da yaso taba wani abu a wata duniya zai iya tabawa, kuma zai ji a jikin sa ya taba abin da kuma samun gamsuwa.