Maganin cutar makanta na farko a tarihin duniya, wanda ke da matukar tsada, maganin idon da kudin shi ya kai dallar Amurka $850,000 dai-dai da naira milliyan dari ukku N300,000,000.
Wannan maganin idon na daya daga cikin magungunan lafiyar jikin dan’adam mafi tsada a duniya. Kamfanin hada magunguna na ‘Spark’ ya bayyanar da cewar ya rage kudin maganin ne daga dallar Amurka milliyan daya $1M zuwa dubu dari takwas da hamsin.
Ganin yadda wasu kamfanonin inshora suka amince da cewar zasu biyama marasa lafiya zunzurutun kudaden, don yi musu aikin ido. Kana da la’akari da yadda tsadar magunguna ta zama ruwan dare, yasa kudin maganin ya ragu.
A watan da ya gabata ne aka amince da maganin na ‘Luxturna’ wanda yake maganin cutar makanta, koda kuwa mutun na dauke da cutar makanta da ya gada kaka da kakanni, wannan maganin zai iya taimakawa wajen warkewar mutun.
Koda kuwa a da mutun baya gani, idan har yayi amfani da maganin anasa ran insha Allah idon shi ya bude.