Babban abinda ke bani matsala a wannan harka ta waka a yanzu kasancewa ta dalibi shine a mafi yawancin lokuta na kan samu aikin yi a daidai lokacin da nake tsakiyar karatu, inji mawaki Usman Abdullahi Nagudu.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Matashin ya yakara da cewa , idan ya samu aiki ya kan ware lokacin da zai yi aiki amma sai kwatsam a saka musu lakca, a irin wannan lokacin ya zama dole ya hakura da sana’ar samun kudinsa ya je makaranta domin daukar darasi.
Ya ce da farko ya fara waka ne domin nishadantarwa daga bisani sai ya lura ana samun kudi a harkar waka, ta hanyar gudanar da tallace tallace.
Usman, ya ce yana illimantarwa sosai ta waka domin kuwa a wata wakarsa da ya fitar wadda ke fadakar da jama’a cewa ba daidai ne ba yadda ake kushe tare da zagin mawaka a cikin a’lumma.
Facebook Forum