Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotu Tayi Umurni Da A Kashe Zakaru 'Yan-Dambe


Wata kutu a kasar Cambodia, ta bada umurnin kashe wasu ‘yan-damben Zakaru, da aka samu a wani haramtaccen gidan dambe. Hukuncin da alkalin ya dauka ya kara jan hankalin jama’a a kasar, wanda ya bayyanar da cewar za’a hukunta masu gidan damben daga baya.

An saka wani hoton bidiyon jami’an ‘yan sanda, wanda ya nuna su a lokacin da suke tattara zakarun da masu zakarun a lokacin aiwatar da umurnin kotun na kashe su cikin jini.

Daraktan kungiyar ‘Transparency International’ kungiya mai rajin kare hakkin bil’adama Mr. Preap Kol, ya rubuta a shafin shi na Facebook da cewar, “Tsarin shari’a na gwamnatin kasar Cambodia kenan, na kashe kimanin zakaru sama da 92 a shekarar 2017”

Ya kara da cewar, wannan daukar alhakine na kashe zakaru da basu san hawaba balle sauka, haka kuma ba’a hukunta wadanda suka munafurci wannan aika-aikan ba.

Ya kara da tambaya cewar “To ina gawarwakin zakarun bayan kashe da akayi?” Wani rahoto a hukumance ya bayyanar da cewar, mahukunta sunyi farfesun kajin kuma sun shanye har romo.

Wasan damben zakaru wasane da aka haramta shi a kasar ta Cambodia, tun a shekarar 2007. Duk wanda aka samu da aiwatar da wasan za’a hukunta shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG