Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana A Kasar Masar Sun Gano Sahun Kafar Fir'auna Bayan Shekaru 4,700


Har ya zuwa yanzu ba’a taba samun kwarangwal din wata halitta a duniya, da takai girman kwarangwal din ‘Fir’auna’ ba, wanda yayi sarauta a daular kasar Masar kimanin shekaru dubu hudu da dari bakwai 4,700 da suka gabata.

Masana binciken tarihin albarkatun cikin kasa, a kasar Masar sun bayyanar da wani sahun kafafun mutun da aka gani a cikin wani kogo, dake yamma ga garin Beit Khallaf a kasar masar da cewar na sarki Fir’auna ne.

Fadi da tsawon tambarin kafar yana nuna wani babban mutun ne ya taba taka wurin, wanda binciken su ya nuna wajen a matsayin fadar fir’auna a wannan zamanin.

Babu wata hallita a duniyar nan da zata bayyanar da wannan a matsayin, sahun mutun a wannan zamanin, don haka yasa suka iya tabbatar da cewar, wannan sahun kafar Fir’auna ne, a lokacin da yayi zamanin da Annabin Allah, Annabi Musa.

Shugaban binciken Francesco M. Galassi, na jami’ar Zurich, dake kasar Switzerland, ya kara da cewar suna kara zurfafa bincike don kara gano wasu abubuwa da zasu tabbatar musu da cewar sarki Fir’auna ya zauna a dai-dai yankin da suka gano sahun kafar shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG