Mujiyar Dusar Kankara Ta Bayyana A Arewacin Amurka

A dai-dai lokacin da wani tsohon dan-jarida Mr. Scott Judd, yake yawon shawagi na daukar hotunan tsuntsaye, a kusa da tabkin jihar Michigan, kyamarar daukar hoton shi, ta dauko hoton wasu tsuntsaye masu ban’alajabi. A karon farko da ya taba ganin farar mujiya, mai rayuwa cikin dusar kankara ke nan a rayuwar shi.

Ga mutane masu sha’awar tsuntsaye a fadin duniya, sukan ga nau’ukan tsuntsaye daban-daban, amma ganin mujiya fara abune da ba kasafai mutane ke sheda sun gani ba.

A duk shekara akan samu milliyoyin tsuntsaye ‘yan gudun hijira, da sukan bar wasu nahiyoyin zuwa wasu, amma wadannan mujiyoyin da suka bayyana, basu kama da wadanda suka fito daga wannan duniyar.

A wannan shekarar, mujiyoyi da dama sun fito daga yankin da yafi kowane yanki sanyi a duniya, can yankin gabashin kasar Canada tsakanin kasashen Finland, Greenland, Norway, Sweden da kasar Rasha. Wadannan kasashen sunfi ko ina tsananin sanyi a fadin duniya.

A cewar Mr. Scott, mazauni birnin Chicago, ta kasar Amurka, wadannan mujiyoyin da ya gani, suna da ban sha’awa fiye da sauran tsuntsaye da mutun zai gani da idon shi. A bana canjin yanayi a duniya zai taimaka wajen kwararar tsuntsaye 'yan gudun hijira a duniya.