Kimanin mutane billiyan 2 ne a fadin duniya ke amfani da shafin zumunta na Facebook, wanda yawan amfani da shafin da mutane ke yi, yasa shafin yake a raye, in badan haka ba da zuwa yanzu shafin ya zama abun tarihi.
Hakan yasa mutane da dama suke mamakin irin kalaman kamfanin, wanda ya bayyanar da illolin amfani da shafufukan zumunta na yanar gizo, mai take “Shin yawaita amfani da shafufukan yanar gizo na da lahani ga rayuwar mutun?”
Kamfanin yayi amfani da wasu daga cikin rahotanni da masana suka wallafar, da suke nuni da illolin amfani da shafufukan yanar gizo, daya daga cikin irin rahotannin wanda ya bayyanar da cewar, mafi akasarin mutane da suka yawaita karance-karancen abubuwan cigaba da suka samu wasu, sai su dinga kallon kansu a matsayin mutane marasa sa’a a rayuwa.
Hakan ya kan haifar da hali na kyashi, hassada, bakinciki, da kokarin saka kai cikin hallin da mutun ba zai iya yima kanshi magani ba. Sau da yawa mutane kan kokarta wajen gasa, da hada kansu da wadan da su kafi su a rayuwa.
Kawai don ganin irin daukaka da aboki ko wanda suke kallo a matsayin da bai kamata ace ya kai nasu ba, kamfanin dai ya ayyanar da yawan kudin shigar shi da suka kai dallar Amurka billiyan 10, wanda yake ganin za’a iya kauda wannan matsalar.
Kamfanin ya kara da cewar, mutane kada su dinga kallon daukakar wasu, don auna zurfin cigaban su a rayuwar yau da kullun. Mutane suyi amfani da shafin na facebook, don sada zumunci da abokai kana da dangin su.
A binciken da kamfanin ya gudanar a jami’ar Carnegie Mellon, wanda ya bayyanar da mutane masu amfani da shafin don sada zumunci, ga ‘yan-uwa da abokan arziki, suna samu rayuwa mai nagarta sanadiyyar amfani da shafin.