Wani ma’aikacin kamfanin Twitter ya dakatar da shafin shugaban kasar Amurka, Donal J. Trump, @realdonaldtrump. Ma’aikacin da zai bar aiki a kamfanin a ranar Alhamis, ya dakatar da asusun shugaban na tsawon minntoci goma sha daya.
An dawo da asusun bakin aiki jim kadan da aka gano hakan, a cewar kamfanin na twitter, sun kara da cewar sun fahimci cewar wani daga cikin ma’aikatan kamfanin ne ya dakatar da shafin shugaban kasar, amma suna zurfafa bincike don gano dalilin hakan.
Kamfanin sun kara da cewar, suna cigaba da bincike da kuma kawo karshen abkuwar wani abu mai kama da hakan a gaba. Shugaban kasar Amurka Mr. Donald Trump, ya shahara wajen amfani da shafin nashi na twitter.
Wanda ake ganin cewar a duk fadin duniya, babu shugaban kasa da yake amfani sha shafin yanar gizo kamar shi, ya kanyi amfani da shafin wajen kaima abokan hammayar shi hari.
Musamman a gabanin zaben 2016 da yayi nasarar zama shugaban kasar, yana da mabiya a shafin nashi na twitter mutane millitan arba’in da daya da dubu dari bakwai.