Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Kauye Nada Rawar Takawa


Abubakar Adam Sanda
Abubakar Adam Sanda

Mutanen karkara ba abinda da za a manta dasu bane dalilin haka yasa na fara harkar waka domin in fadakar da mutanen karakara irin alfanun dake tattare da cigaban zamani.

Abubakar Adam Sanda, mawaki wanda aka fi sani da Mr A sanda, mai wakar hip-hop na Hausa ne ya furta haka inda ya cigaba da cewar kada a bar mutanen karkara a baya a faggen cigaba ga harkar waka da matsalolin barin matasa a baya tare da rashin samun hanyoyin da zasu isar da sakonninsu ya na cikin dalilan da yasa ya shiga harkar waka.

Ya ce ganin cewar yan birni sunyi wa mutan kauye zarra ya sa ya fito daga kauyen Sanda na karamar hukumar Bunkure domin nuna wa alumma cewar suma zasu iya bada tasu gudumuwar ta faggen cigaban matasa

Ya ce matasa na da matsalolin mussamam ma matasa da suka fara wakokin hip-hop mutane na ganin cewar ba salon waka ce ta harshen Hausa ba, sannan ana yi musu kallon sun iyi asara kasancewar sun zabi waka a matsayin sana’a.

Mr A sanda ya ce babban burinsa sakon da yake isarwa ya je wanda suka yi don su sannan ana dai yi musu mummunar kallo da rashin kyautata musu niyyar domin a cewarsa suna tafiya da duniya ne a yadda ta ke.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:22 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG