Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dumamar Yanayi A Wannan Zamanin Ya Haura Na Shekaru 800,000 Da Suka Wuce


Dumamar Yanayi
Dumamar Yanayi

Kungiyar manazarta dumamar yanayi ta duniya “World Meteorological Organization” a turance sun fitar da wani rahoto dake bayyanar da yanayin dumaman yanayin duniya, wanda ya kai ma’aunan gididdiga da aka kwashe sama da shekaru 800,000 ba’a samu irin yanayin ba.

An bayyanar da rahoton ne gabanin taron kwamitin dumamar yanayi na majalisar dinkin duniya, da za’a gabatar sati mai zuwa, a birnin Bonn, kasar Germany. Wannan yana nuni da cewar, kasashen duniya ya kamata su tashi tsaye.

Wajen ganin an tunkari matsalar dumaman yanayi gadan-gadan, domin lokaci baya jiran kowa. A cewar rahoton kungiyar, a karon farko da alkalunma suka bayyanar da zafafar yanayi a doron kasa ya hau matuka.

Domin kuwa an samu karin zafafar yanayi da karin kimanin kashi 145, sama da abun da aka saba samu a tarihin duniya, wannan rahoton kuwa yana nuni da cewar, za’a iya samun munanan yanayi da jama’a zasu wahala matuka.

Karuwar kamfanoni masu amfani da manyan mashina dare da rana, na daya daga cikin dalilan da suke haddasa zafafar yanayi a duniya. A cewar sakataren kungiyar Mr. Petteri Taalas, wannan matsalar yanzu haka tana faruwa, kuma babbar matsalace.

Ya bayyanama VOA cewar, yanzu haka masana sun gano wasu sinadarai da suke haddasa dumaman yanayin, da suka taru a wani guri, wanda suka kwashe shekaru suna taruwa a yankin. Za'a kokarta aga an shawo kan matsalar idan halin hakan ya samu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG