Mutunmutumin tsuntsu ya sauka a farfajiyar jami’ar Michigan a karon farko, tsuntsun mai kafafu biyu, da aka radama suna “Cassie” an kirkiri wannan tsuntsun ne, da zummar kai daukin gaggawa a duk lokacin da aka samu wata annoba.
Masana a jami’ar ta Michigan, sun rada ma tsuntsun suna Cassie wanda aka samo sunan daga ‘Cassowary’ wani tsuntsu da baya tashi sama, wanda yake kama da Jimina. Tsuntsun na da kimanin tsawo na mita daya.
Duk dai da cewar tsuntsun bashi da fikafiki, yana da nauyin kimanin kilogram 29.94 kwatankwacin nauyin fiye da rabin buhun siminti. A jikin tsuntsun, an kayatar da shi da wasu akwatuna, masu rike da na’urar kwamfuta, da duk wasu sinadrai da zasu taimaka mishi wajen gabatar da aiki yadda ya kamata.
Kamfanin Albany suka kera shi, wanda jami’ar Michigan ta siya, kuna da inganta shi. Wannan shine mutunmutumi mai suffar tsuntsu na farko da aka fara kirkira a tarihin mutunmutumi a duniya.
Manazartan sun bayyanar da jin dadin su matuka, da samun nasarar tura tsuntsun don gudanar da irin aikin da aka kirkire shi dan aiwatar wa. Daraktan gudanarwa a tsangayar mutunmutumi ‘Robotic’ na jami’ar Mr. Jessy Grizzle, ya bayyanar da irin jin dadin su a madadlin sauran dalibai da malamai abokan binciken.