Shafufukan yanar gizo na da amfani matuka, ba wai kawai ga matasa ba, musamman idan anyi amfani da su ta hanyar da suka dace. Shugaban kasar Amurka, Mr. Donald J. Trump, ya bayyanar da cewar, badan karfin shafufukan yanar gizo ba, ai kuwa da bai zama shugaban kasar ba.
Kasar Amurka na daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki, da soji a fadin duniya. Shugaban dai ya bayyanar da cewar, wannan wata kafa ce mai karfi musamman wajen aika sakonni da mafi akasarin gidajen jaridu kanji shakkar isarwa a wasu lokutta.
Dalilin shi kuwa na rike wadannan hanyoyin shine, idan gidajen jaridu basa isar da sakon da suka kamata, har idan basu yi dai-dai da tsarin suba, hakan yasa zai yi amfani da wadannan kafofin don isar da sakon shi da kan shi.
Ya kara da cewar, gaskiya badan wadannan kafofin ba, da gaskiya bai kai inda yake ba yanzu, a matsayin shugaban kasar Amurka. Sai ya kara da cewar a duk lokacin da wani yayi wata magana akan shi, batare da bata lokaciba zan dauki wayata na maida martani.
Amma bana amfani da shafufukan wajen aikata wasu abubuwa da basu kamata ba. Wasu ‘yan siyasa na ganin cewar shugaban ya kamata ya daina amfani da shafufukan, wanda har wasu daga cikin abokan shi, suna bashi irin wannan shawarar.
Ana ganin kamar shugaban ya kanyi amfani da shafufukan, wajen kaima abokan gabar siyasar shi hari. Wanda a wasu lokutta bashi da tabbacin abu amma sai kawai ya rubuta a shafin shi da cewar abun ya faru.
Facebook Forum