Kamfanoni da shaguna a fadin duniya na kara zamanantar da shagunan su, da kokarin maye gurbin mutane da na’urorin mutun mutumi, musamman wajen ganin sun gabatar da aikin da ya kamata mutun yayi.
A yanzu haka wasu shaguna suna samar da mutun mutumi mai kwakwalwa kamar ta mutane, zai yi aiki tamkar mutun. Kamfanoni kamar su Amazon, zasu iya zama kamfani da zasu siyar da kayan sawa, a shekara mai zuwa fiye da duk wani kamfani.
Sabo da wani sabon tsari da suka fito da shi, wanda zai bama mutane damar tattaunawa da mutun mutumi, wajen daukar gwajin kayan su. Abu da mutun zai yi shine, ya shiga shafin yanar gizo nasu, zai rubuta tsawon riga, hannu, wando da irin fadi ko girman wuya da yake so.
Bayan yin duk hakan za’a dinka mishi kayan, da kuma isar dasu gidan mutun a cikin lokaci. Hakan ya karasa wasu da dama yunkuri wajen ganin suma ba’a barsu a baya ba, wajen ganin sun kayatar da shafin su na yanar gizo don tallata hajojin su.
A wannan karni da ake ciki, duk wani mai sana’a zai bukaci zamanantar da sana’ar tashi, tahaka ne zai samu karin masu saye cikin kankanin lokaci, musamman idan mutun yana kokarin tallata hajojin nashi a shafufukan yanar gizo, kamar su facebook, whatsapp, Instagram, twitter da dai makamantan su.