Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kyamara Mai Kwakwalwa Zata Nuna Masu Laifi Daga Nesa


Kyamara Mai Kwakwalwa
Kyamara Mai Kwakwalwa

Daya daga cikin yanayi da za’a samar nan da yan shekaru kadan masu zuwa, sun hada yadda motar ‘yan sanda zata iya nuna masu laifi, ko kamun matukin motar yaga mai laifin. Wannan wani yunkuri ne da wani kamfani keyi.

‘Coban Technology’ kamfani ne da suka shahara wajen samar da kyamarar motacin jami’an tsaro, a birnin Houston dake jihar Texas ta kasar Amurka. A satin da ya gabata, sun sanar da cewar zasu kaddamar da wata kyamara, wadda zata hangi mutun daga nesa, kuma ta bayyanar da duk wasu bayanai da suka shafi rayuwar shi.

Kyamarar mai kwakwalwa, bata da yawa, za’a fara amfani da ita don gwaji, wajen bama jami’an tsaro damar kama masu laifi a kowane lokaci. A duk loacin da aka samu mutun da wani laifi, kuma ya gudu, duk inda kyamarar ta hango shi zata bayyanar.

Za’a saka bayanan shi a cikin kwamfatar jami’an tsaro, wanda kyamarar za’a daurata a jikin mota. A duk loacin da jami’in tsaro ya kusanci mai laifi, kyamarar zata nuna mishi cewar, akwai mai laifi wane kaza, da ake nema da aikata laifi kaza.

Kyamarar za’a inganta ta da wasu sinadarai da zata iya bayyanar da inda ake ajiye wasu makamai, kamar su bindiga kodai a jikin mutun ka a cikin mota, kyamarar na iya zagaye mota don ganin abun dake faruwa a kowane bangare, matakin 360.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG