Akwai tabbacin cewar, halittun cikin Tuke zasu fuskanci matsalar iska, sanadiyyar gurbatacciyar iska da ake samu daga rayuwar yau da kullun a cikin birane. Binciken da aka kwashe shekaru 8 ana gudanarwa, da ya hada da manazarta kimiyya mutane 250.
Binciken ya tabbatar da cewar, halittu dake cikin teku baza su dinga samun nagartacciyar iska da zata basu damar walwala ba, da kuma basu damar saka kwai da kyankyashe su cikin lafiya.
Hakan na nuni da cewar, za’a iya samu karancin halitun cikin ruwa a nan da shekaru kadan masu zuwa, yawan ‘yaya ko kwai da halittun zasu dinga sakawa, zai ragu matuka. Haka tsofaffi zasu dinga mutuwa cikin kananan shekaru.
Sakamakon binciken ya tabbatar da cewar, ana iya samun karancin hallitun ruwa da mutane kan iya ci, saboda matsalar rashin walwala ga halittun. Jiragen ruwa da ke shawagi a cikin teku, suna kara taimakawa wajen karuwar gurbatar iskar da hallitun ke shaka.
A lokutta da yawa, jiragen kan fesar da bakin mai cikin teku, hakan na shafar lafiyar ruwan da halitun ciki.
Facebook Forum