Kamfanin Facebook Na Wani Yunkuri Na Kasa Shafin Gida Biyu

Shahararren kamfanin zumunta na Facebook sun fara wani sabon gwaji don raba shafin nasu gida biyu, inda suke kokarin ware bangaren tallace-tallace da bangaren labarai. Wanda suke ganin kamar hakan zai kara sa ‘yan kasuwa su yawaita amfani da shafin wajen tallata hajojin su.

Kamfanin dai da yayi fice a duniya, wajen sada zumunta a yanar gizo, sunce wannan tsarin zai taimaka ma mutane, da kanyi amfani da shafin wajen aikawa da sakonni ga dangi da suke wasu nahiyoyin.

Mutane da yawa sukan saka hotunan su, kayan kasuwanci, haka da mutane da suka shahara, kodai mawaka, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa, da dai makamantan su, zasu dinga amfani da damar wajen saka duk wani abu da suke so.

Su kuwa masoya wadannan shafufukan zasu tafi kai tsaye, bangaren da suke da bukatar samun duk wani bayani da suke bukata. Gwajin dai za’a fara shi ne a wasu kananan kasashe guda shida, inda mutane zasu samu damar shiga shafin ta bangarori biyu.

A cewar kamfanin, bangaren farko, zai shafi rayuwar mutun da dangin shine kawai, dayan kuwa, zai shafi ire-iren shafufuka da mutun ya taba nuna kaunar shi gare su.

A duk lokacin da mutane ke da bukatar a ga hajojin su, ko wani labari da suke da shi, kuma suke so kowa ya gani, zasu biya kudi domin labarin ya bayyana a bangaren labaran dangin mutane.

Za’a fara gwajin a kasashen Bolivia, Cambodia, Guatemala, Serbia, Slovakia da kasar Sri Lanka, wanda ake sa tsanmanin gwajin zai dauki tsawon wasu watanni. A cewar shugaban tallace-tallace na kamfanin facebook Mr. Adam Mosseri.