Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ga Masu Bukatar Zama Amurkawa, Lokacin Gasar Samun "Green Card" Yayi


Baki daya duk wasu bayyanai da mutane suka shigar, a shafin shirin gwamnatin Amurka, na bama mutane a fadin duniya damar zama ’yan kasar. Tsarin da akema take ‘Green Card Lottery’ tsari ne da yake ba mutane a ko ina a fadin duniya, damar zama halittatun Amurkawa.

A duk shekara gwamnatin kasar Amurka, na fitar da wasu ka’idoji da mutane zasu cika don shiga cikin tsarin, mutane daga kowace kasa zasu iya shiga cikin gasar. A wannan shekar an samu wata ‘yar karamar tangarda, wanda yasa duk wanda ya shigar da bayanan shi a shafin, aka bukaci da ya sake shigarwa.

Tun daga ranar 3 ga watan Oktoba na wannan shekarar har zuwa 10 ga wannan watan, shafin hukumar dake kula da gasar, ya samu matsala. Don haka duk wanda ya shigar da bayanan shi, ana bukatar ya sake shigarwa daga ranar Laraba 18, ga wannan watan har zuwa ranar Laraba 22, ga watan Nuwamba 2017.

Daya daga cikin ka’idojin shiga gasar shine, kada mutun ya cika fom din shiga gasar sau biyu, amma sabo da matsalar da aka samu, duk wanda ya san da cewar ya shigar da bayanan shi a wadannan ranakun daga 3 zuwa 10 ga wannan watan, zasu iya sake shigar da bayanan su.

Ga kuma wadanda suka samu nasarar shiga gasar, za’a aiko musu da wani sakon email da zai basu karin haske. A cewar mai magana da yawun hukumar Mr. Pooja Jhunjhunwala, ta bayyana ma gidan radiyon Muryar Amurka VOA, cewar suna bama mutane hakuri da wannan tangardar da aka samu, kuma mutane suyi amfani da wannan damar don sake cika bayanan su.

Kuma zasu sanar da ofisoshin jakadancin Amurka da suke a kasashen duniya, da suyi ma jama’a karin bayanin abubuwan da suka faru. Domin kuwa mutane da suka fito daga kasashe masu tasowa, basu samu damar duba yanar gizo balle su san abun dake faruwa da fom din su.

Ga duk wani mai sha'awar shiga shirin don zama halittacen dan kasar Amurka, zai iya zuwa wannan shafin don cika nashin bayanan, www.dvlottery.state.gov

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG