Kimanin shekaru biyu kenan da suka gabata, da wani mahalbi dan kasar Amurka Mr. Walter Palmer, ya kashe rikakken zakin da ake alfahari da shi a kasashen Afrika, mai suna ‘Cecil’ a cikin dajin namun dawa dake kasar Zimbabwe.
Kwatsam sai ga hakan ya abkama dan shi Xanda, mai shekaru shida da haihuwa. Labari ya isa ga mahukunta cewar an kashen zakin tare da wasu jariran zakuna, an ruwaito cewar an kashe shine a gabar dajin Hwange.
Wasu masana a jami’ar Oxford dake kasar Birtaniya, sun sakama zakin wata na’ura da take nuna duk inda zakin yake, a cewar Mr. Andrew Harding, tun zakin na dan shekaru kadan, amma an samu wasu da suke farautar shi.
Ana kuma sa tsanmanin cewar mafarautan sun fito daga kasashen Amurka, Birtaniya da Afrika ta kudu, inda suke kokarin bada abun goro na makudan kudade don sayan gawar zakin.
Ya zuwa yanzu dai ba’a samu rahoton suwa suka kashe zakin ba, wasu kwararru suka bayyanama mahukunta rasuwa, kuma suka mika gawar shi ga masu tsaron gandun dajin.