Dr Shamsudeen Ahmad, dan Najeriya mai karatun digirin digirgir a Phd. Fannin likitanci a jami’ar Hull da ke Ingila, ya sami tattaunawa da Yusuf Aliyu Harande, a shirin ilimi da dandalinvoa ke gabatarwa a a kowace ranar Litini da Alhamis.
Kamar yadda muka saba jin ra’ayoyi da sakonni zuwa ga matasa daga wurin kwararru a fannoni daban daban, a wannan karon, Dr Shamsuddeen yayi Magana ne musamman akan yadda ake fama da matsalar karancin likitoci musamman mata a arewacin Najeriya.
Da yake ci gaba da bayani, likitan ya fara bayani akan yadda dalibai da dama ke razana da rashin samun kwarin gwiwar shiga fagen karatun likitanci, da kuma irin halin da al’umma kan sami kanta sakamakon irin wannan matsala.
Jama’a da dama na fama da rashin lafiya iri daban daban, amma rashin isassun likitoci yasa da dama basa samun magungunan da suka dace a kan lokaci, wasu maza da dama kuma basa bari matansu su je asibiti sakamakon rashin likitoci mata da zasu duba su.
Ko ta wacce hanya za’a iya shawo kan lamarin?, Dr Shamsudeen, ya bada shawarwari ga matasa maza da mata masu shi’awar karatun likitanci, da kuma kira ga al’umma domin bada goyon baya ga matasa masu shi’awar wannan karatu.
Domin cikakken bayani, saurari hirar a nan.
Facebook Forum