Kimanin shekaru arba’in da takwas kenan da suka gabata, da Mr. Buzz Aldrin, shine mutun na farko da ya taba fara tafiya a cikin duniyar wata. ‘Apollo 11’ wanda akafi sani da ‘Kunbo Affolo’ A shekaran jiya ne aka gudanar da bukin tunawa da wannan ranar da irin bajintar shi.
Kimanin sama da mutane dari hudu ne suka halarci wannan taron, da aka gudanar a dakin taro na tunawa da tsohon shugaban kasar Amurka margayi Kennedy Space Center. Shi dai Mr. Buzz mai shekaru tamanin da bakwai, ya kaddamar da bukin tunawa da shekarar 1969, wanda aka dauki burin zuwa duniyar sama.
Mr. Buzz, ya kaddamar da gidauniyar ilimin duniyar wata, inda aka tara kudi kimanin dallar Amurka $190,000. Yana kuma da yakinin cewar nan da zuwa shekarar 2040, mutane zasu isa duniyar wata, kana zasu iya yin abubuwa da dama a duniyar.
Gidauniyar ta fara kirkirar jirgi don zuwa duniyar ta wata, da ake sa ran wasu Amurkawa zasu tafi, ya kara da cewar a shekarar dai mutane goma sha biyu ne suka shiga duniyar watan. Yayi godiya ta musamman ga daukacin mutanen da suka taimaka wajen samun nasarar wannan jan aikin.