Idan har ba’a samun wadatacciyar wutar lantarki, duk wasu kayan kimiyya da fasaha, kamar su wayar hannu, kwamfutoci suna iya zama aikin banza. Wannan wani abune mai sauki, wanda a lokutta da yawa ba’a basu kulawa da suka kamata.
Musamman a kasashen da suke tunkaho da cigaba, a kimiyya da fasaha. Amma su kuwa kasashe masu tasowa, wannan ba wani abun tada hankali bane. Domin kuwa kafofin samar da yanar gizo nazama babbar matsala a garesu.
A duk lokacin da akace mutane na fama da matsalar wutan lantarki, to za’a ga cewar damuwar su ba wai abasu yanar gizo bane, sunfi maida hankali wajen ganin sun samu ingantacciyar wutar lantarki, ruwan sha, da magani.
A cewar daraktan samar da yanar gizo a kamfanin Microsoft Mr. Paul Garnett, a yayin da yake magana akan tsarin samar da yanar gizo da kayan kimmiya da fasaha masu rahusa ga kasashe masu tasowa.
Sai yace, shekaru biyu da suka wuce kamfanin ya kaddamar da tsarin samar da yanar gizo mai rahusa. Wanda aka ware zunzurutun kudade da suka kai dallar Amurka $75,000 zuwa $100,000 ga kamfanoni 10, wanda duk kamfanonin sun samu kayan aiki daga kamfanin na Microsoft.
Muhimancin yanar gizo ga al’umar duniya, yakai kamar muhimancin abinci da muhalli, domin yanzu haka daukacin mutane da suke duniya, akwai sama da mutane billiyan 3.9 da basu samun yanar gizo.
Wanda hakan babbar ill ace ga cigaban duniya da ma rayuwar mutane. Domin ta amfani da yanar gizo, za’a iya kawar da talauci, cututuka, ta’addanci, jahilci, da dai makamantan su. Musamman idan mutane sunyi amfani da yanar gizon ta yadda ya kamata.
Facebook Forum