Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsibirin Kankarar 'Antarctica' Mafi Girma A Duniya Ya Tsage


Tsibirin kankara mafi girma a fadin duniya ya tsage biyu, tsibirin da ya mamaye yankin Antarctica, yanki da yafi ko’ina sanyi a fadin duniya, da kimanin murabba’in kilomita 6,000.

A jiya Laraba ne na’urar tauraron dan’adam ta kasar Amurka, ta hango tsagewar, a yayin da take shawagi a yankin da akema lakani da ‘Larsen C Ice Shelf’ masana sun bayyanar da cewar da jimawa sun tsanmani abkuwar hakan.

Tun a shekarar 2014, aka tsanmani tsagewar kankarar, kankarar ta kwashe tsawon sama da shekaru goma a hade, wadda take da kaurin ma’auni milimita 200, alamu dai na nuna cewar kankarar zata dauki lokaci mai tsawo kamun ta narke.

Yanzu haka kankarar na matsawa kusa da yankin Arewa da kogin Antarctica, wanda idan hakan ya faru, tana iya zama barazana ga jiragen ruwa. Masanan sun kara da cewar ruwa a yankin ya fara yin dimi, wanda iskar dake kadawa a yanki tana da sauran sanyi, a matakin kasa da ziro.

Tsaguwar dai bata bayyana kwarai ba a wannan satin farko ba, amma ga dukkan alamu kankarar tafara narkewa, a cewar Farfesa Adrian Luckman, na jami’ar Swansea, wanda ke bibiyar nasarar da kankarar ke samu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG