Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Zasu Inganta Manhajar Sakon Gaggawa Da Tallace-Tallace


Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg
Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg

Kamfanin Facebook, sun bayyanar da yunkurin su na inganta manhajar su ta aika sakon gaggawa ‘Messenger App’ inda mutane zasu iya amfani da tsarin wajen tallata hajojin su.

Kamfanin da shine na daya a duniya da ya shahara a fagen yanar gizo. Nan bada jimawa ba, zasu siyar da hannun jarin wannan manhajar, ana iya ganin aikin manhajar, mutane zasu dinga ganin tallace-lallace a gaban shafin manhajar nasu.

A duk lokacin da mutun ya danna sabon tsarin, zai kai mutun kai tsaye ga tallar ko kuma shafin kamfanin abun da yake da bukatar siya, ko kuma mutun zai iya shiga cikin tsarin ganawa kai tsaye da mutanen kamfanin, da yake da bukatar siyan kayan su.

Hakan ya biyo bayan gwajin manhajar da kamfanin yayi a kasar Australia da Thailand a watan Janairu, kamfanin dai yana ba ‘yan kasuwa sama da billiyan 1.2 damar ganawa da abokan hurdar su a duk wata.

Kanfanin dai na samu kashi 85% na kudin shigar su ne ta hanyar amfani da tsarin waya, amma idan suka inganta wannan tsarin, zai taimaka musu wajen kara samun kudaden shiga. Don haka yasa suka fito da sabon tsarin, don jin dadi da saukin rayuwa ga jama'a.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG