Hare-haren ta’addanci sun kashe mutane fiye da dubu 20 kai tsaye a nahiyar Afirka cikin shekaru biyar da suka shige. Kungiyoyi guda biyu, watau Boko Haram da al-Shabab, sune suka kashe 71 cikin 100 na wadannan hare-haren.
Haka kuma wadannan kungiyoyi guda biyu, sune suka kashe kashi 91 cikin 100 na wadannan mutanen.
Amma duk da yake har yanzu akwai wadannan kungiyoyin guda biyu, yawan mace-macen da suke haddasawa zai ci gaba da raguwa a shekara ta biyu a jere a bana, inda a wannan shekara yawan hare-harensu ya ragu sosai idan an kwatanta da shekarar 2012, shekarar da abin ya fi tsanani.
Wannan sakamakon yana kumshe ne a cikin bayanan da VOA ta bi diddiginsu daga wata hukuma da ake kira ACLED a takaice, wadda take bins awun duk wani harin da aka kai da makami, da wurin da aka kai da kuma irin barnar da aka yi a nahiyar Afirka. Irin hare-haren da hukumar take bin sawu sun hada da na ta’addanci, da na siyasa da kuma wadanda suka shafi zanga zanga.
Alkaluman da wannan hukuma ta ACLED ta tattara sun samo asali tun daga shekarar 1997, kuma ta kan yi hakan ta hanyar nazarin duk wata kafar labarai a inda abu ya faru, da bayanan da gwamnati ke bayarwa, da wadanda kungiyoyi masu zaman kansu ke tattarawa da kuma binciken da ake gudanarwa a wallafa kan dcuk wani rikici ko tashin hankali.