Kungiyar bada agaji ta Red Cross tace mutane ukku ne – da suka hada da Amurkawa biyu da wani dan kasar Spain guda - shanu suka ture kuma suka ji musu rauni yau Jumu’a a lokacin tseren shanu da aka yi a birnin Pamplona dake can kasar Spain.
Kungiyar bada agajin tace dan kasar Spain din ne, 46, yafi jin jiki, inda har ta kai saida aka yi mishi aikin tiyata don dinke raunukkan da ya samu a kansa da kuma kafarsa. Sauran Amurkawan biyu nasu raunin da sauki, don ance dayan Sa ya ture shi ne a mararsa, daya kuma a duwawunsa.
Wannan wasan tseren shanu dai ya samo asali ne tun shekarar 1926 (shekaru 91 da suka wuce) lokacinda wani shahararren marubuci mai suna Ernest hemminway ya bada bayanin wasan a cikin wani litaffensa da a turance ake kira "The Sun Also Rises.”