Dan Wasan Tennis Federer, Ya Sake Shiga Gasa Da Nasara

Shahararren dan wasan Tennis Roger Federer, ya sake daukar azama, wajen lashe kambun ‘Wimbledon’ a wasan da suka gwabza da abokin hamayyar shi Alexandr Dolgopolov, inda ya tsere da rauni.

Jim kadan bayan fara wasa Federer ya saka kwallaye 6-3 inda abokin shi ya tashi 3-0 a cikin mintoci 43 Alexandr ya ajiye wasa, saboda radadin ciwon da yaji.

A cewar Federer, yana farincikin sake dawowa, bayan lashe wasa da yayi a kasar Ingila a zagaye na 85. Yanzu haka dai yana shirin sake karawa da daya daga cikin zakaru da zasu hada da Dusan Lajovic, ko Serbia ko Greek don dauke zagaye na 32.

Dan wasa Dolgopolov, ya nemi tsayawa da wasan a zagaye na farko, biyo bayan rauni da ya samu a idon kafar shi, amma dai ya daure har sai da aka kai zagaye na biyu, bayan minttoci 40.

Wannan bashi ne karo na farko ba da dan wasan ya fita daga cikin jerin wasanni ba, duk dai da cewar yana fuskantar rashin lafiya a cikin wannan shekarar.

Dan wasa Federer mai shekaru 35, yana burin lashe kambu a zagaye na 19th wanda idan yasamu nasarar hakan, zai iya zama mutun na farko mai yawan shekaru da ya lashe kambun a wasannin kungiyar kasar Ingila. Hakan kuma na nuni da cewar, zai sake daukar kambun bayan irirn nasarar da yayi a shekarar 2012.