Amazon Sun Inganta Speaker Don Wayar Bidiyo

Kamfanin siye da siyarwa na yanar gizo Amazon, sun inganta na’urar su ta sauraren magana da kide-kide, sun inganta speaker su, da sashen 'sorftouch' da mutun zai taba cikin sauki tayi magana, ko zabo wakar wani mawaki.

Ita dai wannan sifikar ana iya dabara da ita, ko kuma ana iya hadata da sauran na’u’rorin gida, wanda zata juya abubuwa da zarar mutun yayi mata magana, wannan wani yunkuri ne da suka fito da shi.

Biyo bayan abokan hamayyar su Google suna kokarin wuce su a kimiyyar fasaha. Akwai mutane sama da milliyan 36, da suke amfani da wannan na’urar, wajen hada duk wasu kayan sadarwa a gidajen su, kamar hitar dumama daki, kofofi masu dauke da na’urar maganin barayi. Kana ana iya yin amfani da sifikar wajen waya na bidiyo.

Duk wani abu da mutun ke bukata a cikin gidan shi, zai iya hadawa da wannan na’urar, don ganin kimiyya da fasaha a kusa. Kamfanin zasu kara da wani kokarin su na ganin sun samar da na’urar Alexa a wayoyin hannu.