Gwamnatin China, Zata Kara Matakan Tsaro Wajen Amfani Da Yanar Gizo

Gwamnatin kasar China, zata kara daukar kwararan matakai, wajen duba da bada tsarin yadda jama’a, a kasar zasu dinga amfani da shafufukan su na yanar gizo. A jiya ne Lahadi hukumomi suka bayyanar da cewar, gwamnatin bazata yadda mutane su dinga amfani da shafufukan yanar gizo yada suke so ba, batare da gwamnati ta bibiyi yadda suke amfani da shafufukan ba.

Shugaban kasar China Xi Jinping, yana daukar damarmakin da ‘yan kasar ke da, na amfani da shafufukan yanar gizo, batare da sanin abun da suke iya gani ba, kan iya zama barazana ga gwamnatin shi. Haka kuma akwai tsari da dole ‘yan kasar su bi, wajen tattauna wasu matsaloli a shafufukan su na yanar gizo.

Gwamnatin ta fitar da wani sabon tsari, da zai takaita yadda ‘yan kasar zasu dinga amfani da yanar gizo na tsawon shekaru biyar. Hakan ya hada da yadda ‘yan jarida ke aikin su wajen yada labarai, da duk wasu mutane da suke da mu’amala da yanar gizo wajen aikin su da sana’a.

Ya kara da cewar, ta hakane kawai za’a iya magance matsalar, labaran kanzon kurege, labarai da kan iya tada zaune tsaye, da duk wasu abubuwa da zasu iya zama cutarwa ga ‘yan kasar. Shugaban Mr Xi, yace dole ne ‘yan jarida subi ka’idoji da basu sabama gwamnati ba, wajen bada labara masu inganci da sahihanci. Wannan dai ba wani bakon abu bane a kasar ta China.