An gudanar da bikin AMMA award a masana’antar shirya fina-finai na Kannywood ,inda aka baiwa wadanda suka taka muhimmiyar rawa a masana’antar ta kannywood, kambin girmamawa kama daga mawaka zuwa masu shirya fina-finan da ma jarumai.
Kadan daga cikin wadanda suka sami kambi akwai- ‘Best adopted tv scene play inda fim din ‘Yar Madabo ya samu nasarar, sai Best visual effect fim din ‘Mutum da aljan ya samu nasara.
Best make-up movie kuwa ya je ga fim din Kasko sai Best short fim inda fim din Mutuwar Tsaye ya lashe gasar.
Akan wannan batu ne DandalinVOA ya samu zantawa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar MOPPAN wato Murtala Balarabe Baharu na nasarori da ma kurakuran da aka fuskanta a yayi bikin wannan karamawa da aka yiwa jarumai, mawaka da ma fina finan kansu.
Ya ce a gaskiyar zance an samu cigaba idan aka kwatanta da bara, hakan na baiwa masana’antar kwarin gwiwa wajen inganta abubuwan da suke yi tare da kara masu kaimi, ya kara da cewa duk kuwa da nasarori ba za’a rasa wasu kurakurai ba
Ya ce akwai tsari wajen tantance wadanda suka samu nasara, sai dai ya ce akwai karanci jama’a da suka hallarci taron, wanda yake da nasaba da rashin tallata bikin sai kuma yar matsalolar tangardar na’ura da aka ci karo dashi yayin gudanar da bikin a masana’antar, ta Kannywood.
Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar