Bincike: Sigari Zata Kashe Mutane Miliyan 8, Ta Haifar Da Ribar Dala Biliyan Dubu!

Taba Sigari

Rahoton hadin gwiwa tsakanin hukumar lafiya ta duniya “WHO” da tsangayar binciken cutar Kansa “National Cancer Institute” sun fitar da wani rahoto, dake bayani akan illolin shan taba sigari.

Rahoton na cewa, shan taba sigari na dukufar da tattalin arzikin duniya, wanda ake kashe fiye da dallar Amurka billiyan daya $1B a shekara. Hakan kuma na nuni da cewar nan da shekarar 2030, cutar da ake dauka sanadiyar shan taba, zata kashe kimanin kashi daya %1 cikin uku na mutane mashaya taba.

Kimanin kudin jinya da ake kashema cutar shan taba sigari ke haifarwa, ya zarce kudaden haraji, da kamfanonin tabar ke biya a fadin duniya. Don kuwa kamfanoni na biyan sama da dallar Amurka billiyan dari biyu da sittin da tara $269B, dai-dai da naira tiriliyan tamanin da biyu.

Ana sa tsanmanin cewar mace-mace da ake samu a sanadiyar shantaba, zai haura mutane milliyan shida, wanda zai kai sama da milliyan takwas a shekarar 2030, hakan kuma zai fi karfi a kasashe masu tasowa.

Kusan sama da kashi tamanin 80% na mashayan, sun fito daga kasashe masu tasowa ne, duk da hakan karuwar shan taba sigari na kara hauhawa a fadin duniya.

Rahoton ya kara da cewar, shan taba itace cuta daya tilo, da ke haddasa cutar kansa da mutuwa cikin gaggawa da kuruciya. Kuma shan taba ne kawai ake kashema sama da dallar Amurka billiyan daya wajen kiwon lafiya a fadin duniya.