Likitoci Na Yunkurin Samar Da Hantar Roba, Ga Masu Cutar Sankarar Hanta!

Cutar Sankarar Hanta

Taron likitoci na gabatar da wani bincike, don fito da wata hanyar magance cutar sankarar hanta. Ga duk masu dauke da cutar, za’a iya samar musu da hantar roba. Suna ganin cewar idan sukayi hakan, hakan zai bama masu dauke da irin cutar, damar zama kamar sauran mutane.

Mafi akasarin maganin cutar sankarar hanta, shine a dasama mutun wata hantar da akan iya cirowa daga jikin wani mutun. Suna ganin wannan wata babbar matsala ce, musamman ga duka mutane. Baya ga shan wani magani da zasu dingayi, har iya tsawon rayuwar su.

Domin a wasu lokutta hantar da akan dasa ma wasu, bata karbar jikin wasu, wanda hakan yakan iya zama sanadiyar mutuwar mutun biyu madadin daya, da mai badawa da mai karba. Don haka suna ganin cewar idan suka samar da wata hanya mafi sauki, abun sai yafi bada ma’ana.

A cewar Farfesa Kattesh Katti, na jami’ar Missouri, wanda ke jagorantar binciken, ya bayyanar da yunkurin su na ganin sun saukaka hanyoyin magance manya-manyan cututtuka a duniya. Wanda suka hada da samar da wani magani, da zai yaki cututtukan da kan addabi wasu sassan jikin dan’adam.