A shirin mu na nishadi, yau mun sami bakuncin mawakin hip-hop, wanda aka fi sani da Gambara da Hausa, wato - Mohd Zahid wanda aka fi sani da suna Mzee-ice, ya ce ya fara harkar waka ne sanadiyar rawa da yake tare da wani uban gidansa, wanda ya koya masa yadda ake hada waka da kida.
Abokin nasa ne ya bashi shawarar shiga harkokin waka, ganin yadda yake bin kida yana kuma rawa, inda ya bayyana masa cewa zai yi kyau idan ya maida hankali kan rera waka.
Duk da yake ya fara ne da gasa da ake yi ta mawaka da masu rawa da kamfanin Maltina ke daukar nauyi, daga haka ne ya tsinci kansa a harkar rawa da waka.
Babban burin Mzee-ice dai shine yaga ya sami kansa cikin manyan mawaka na Rap a duniya, ya kuma kara da cewa yawanci mawaka irinsa na isar da sakonni ga al’umma musaman ma matasa, baya ga nishadantarwa, yana kuma wa'azantar da mai sauraro.
Daga karshe ya bayyana cewa rawar da yake yi a lokacin da yake rera wakar hip-hop, tana kara bashi azama da dama da kuma basirar rero waka mai ma’ana.
Ga hirar Baraka Bashir da Mzee-ice
Your browser doesn’t support HTML5