Samari sai a maida hankali, akan wasu abubuwa da zasu samo muku girma a wajen ‘yan-matan ku. Sau da dama matasa kan shiga runbun soyayya, da har sukan aikata wasu abubuwa ga ‘yan-mata, ba tare da suna cikin hayyacin suba.
Wadansu abubuwa da samari kanyi ma ‘yan-matan su, da suke ganin kamar suna burge ‘yan-matan, amma su ‘yan-matan suna ganin samari kamar basu san abun da su keyi ba. Kada zafin soyayya ya kwashe saurayi ya biyama budurwa kudin makaranta, ba’ana nufin kada mutun ya nuna son shi, da kauna ga mace da kuma harkar karatun ta ba. Sau da yawa samari kan kashe kudi a kan mace, sai ta gama karatu sai ta watsar da shi, ta kama wani sabon saurayin.
Kada ka siya wasu kaya masu tsada don burge budurwa, bayan tana da masaniyar baka da karfin siyan kayan, hakan na iya zama sanadiyyar ta rainaka, idan ta gane cewar bashi kasiyo kayan, haka kada saurayi yayi zamba cikin aminci, duk dan ya samu kudin da zai burge budurwa. Hakan zai kara saka shi cikin halin wahala idan budurwar ta yarda shi.
Kada kayi fada akan budurwa, ko saurayi ya rabu da aboki ko kawa, saboda budurwa tace batason abokin, ko rashin kyautatawa tsakanin ka da wasu akan budurwa, shima kuskure ne. Haka kada budurwa tasa saurayin canza surar jikin shi, ko dai tace batason yadda gashin kanshi yake, ko tanason taga yayi wani abu da zai sa shi cikin wani hali na damuwa daga baya.
A takaice gaskiya itace maganin duk wata matsala a rayuwa, ganin yadda matasa kanyi amfani da shafufukan sada zumunta na zamanin, kamar su facebook, twitter, Instagram, whatssapp, dai dai makamantan su, wajen karya da sace-sacen basira. Wannan baya haifar da komai ga matasa, sai kaskanci da komawa baya a cikin sa’o’i.