Shafin zumunta na “Twitter” sun fitar da rahoton labarin da akafi tattaunawa a shekarar 2016. Babban labarin da aka tattauna shi a tsawon lokaci a fadin duniya, shine labarin wasannin Rio Olympics, shine labari daya tilo, da billiyoyin mutane a ko ina a duniya suka tattauna lokaci daya.
Labari na gaba kuwa, shine labarin zaben kasar Amurka, wanda dan takarar jam’iyar hamayya Donald J. Trump, ya lashe zaben, inda yayi ma Uwargida Hillary Clinton kaye. Labari na uku kuwa shine labarin wasan game mai suna “Pokemon Go” wanda aka kaddamar a tsakiyar shekarar 2016, shima ya samu zantawa matuka.
Na hudu kuwa, shine wasan zakaru na kasashen turai “Euro2016” wanda ‘yan wasan kasar Portugal, suka lashe kambu. Na biyar kuwa shine kyautar “Oscars” wanda ake bama, ‘yan wasan fina-finai ko mawaka da dai fitattun mutane.
Duk dai a cikin wannan shekarar ne, kamfanin na twitter suka kara sararin rubutun su, da ya kai harrufa dari da arba’in 140, haka kamfanin dai sun samu raguwar abokan hurda, inda kamfanin facebook, da Snapchat, su kayi musu zarra.