Maryam Tafida Bello, shugabar kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Girl Child Engage, wadda ke jagorantar wani shiri da ke duba yadda ‘ya’ya mata ke gudanar da ayyuka na musamman dangane da ilimin diya mace.
Kungiyar ta fara gudanar da shirinne bayan da aka gudanar da wani shiri akan labarin wasu mata su tara a faifan bidiyo, inda aka bada labarinsu na gaske wanda shi ya hassasa samar da wannan shiri domin kawar da matsalolin mata, tare da muhimmanci basu ilimin boko.
Shugabar ta kara da cewa, a fadin duniya bakidaya, yara miliyan sittin da biyu ne basa zuwa makaranta, yayin Nijeriya ke da miliyan goma na 'ya'ya mata da basa zuwa makaranta, inda mafi yawancin wadannan yara sun fito ne daga arewacin kasar.
Ta kuma kara da cewa kungiyar tasu na amfani da wannan labarin da suka hada na bidiyo domin wayar da kan iyaye mata dangane da muhimmancin ilimin diya mace tare da tattauna matsalolin dake tattare da su .
Suna samun cigaba mai yawa, ta inda suke samun hadin gwiwa daga sauran kungiyoyin cigaban mata.