Mawaki Ali Isa, wanda aka fi sani da Ali jita- ya ce babban kalubalen da suke fuskanta shine rashin kishi irin na malam Bahaushe na kyamatar harensa da kuma aron harshen Turanci don su burge al’umma wanda a cewarsa kalubale ne da ke ci musu tuwo a kwarya.
Ali Jita ne ya bayyana haka a tataunawarsa da wakiliyar DandalinVOA, inda ya ce ta amfani da wake ne suke kokarin inganta harshen Hausa, mussamam ma ga Hausawan da aka Haifa a wasu kasashen.
Ya kara da cewa ya fara waka ne shekaru goma sha biyar da suka wuce a matsayin sha’awa kamar yadda kowanne mawaki ya fara, hakazalika kuma ya fara koyon waka ne tun daga makarantar islamiya.
Mawakin ya bayyana cewa ya kwaikwaiyi amfani da Jita ne sakamakon kaunar da yake yi wa mawaki dan kasar Nijer marigayi Sa’adu Bori, a hakan ne har shima ya samu nasa salon.
Ko da yake Allah bai bashi damar gudanar da waka tare da gwarzon nasa ba amma a cewarsa sun taba yin wasa a tare.
Daga karshe ya ce ya gamsu da sana’ar da yake yi a yanzu, ya ce a baya yayi wa ‘yan fina-finai waka amma a yanzu ya fi raja’a ga wakokin jama’a Kuma yana da burin bude record level da zai taimaka wa kananan mawaka.
Your browser doesn’t support HTML5