Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abinda Zai Biyo Bayan Boko Haram Zai Yi Muni Idan Ba’a !


Wani kididigar Banki duniya ya danganta talauci da rigingimu irin na Boko Haram, rahoton na bankin duniya na nunu da cewa yankin arewa maso gabashin Najeriya, da kasar Chadi da Kamaru da yankin Dafur dake kasar Sudan da kuma kasar Nijar, sune yankunan da suka fi talauci a wannan bagare na duniya.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shattima, ne ya furta haka a lokacin da kwamitin sa ido kan yadda aka kashe kudaden da aka kebewa ‘yan gudun hijira, karkashin jagorancin sanata Shehu Sani, suka ziyarce shi a gidan Gwamnati.

Ya kara da cewa magance matsalar talauci da samar da ingantatcen ilimi, ga al’umar yankin arewa maso gabashin Najeriya, shine zai magance rigingimun ‘yan kungiyar Boko Haram.

Gwamnan ya ce idan ba’a magance matsaloli kamar na matsanancin talauci da ake fama dashi ba da kuma bunkasa harkar ilimi ba ga marasa galihu, to abinda zai biyo bayan rikicin Boko Haram, zai yi muni idan ba’a maida hankalin kan wadannan batutuwaba.

Yace duk yake ba abin alfahari bane kashi tasa’in na ‘yan gudun hijira dake wannan kasa daga jihar Borno, suke harma wadanda suke garin Adamawa, duk ‘yan jihar Borno ne.

Amma saboda irin abinda za’a samu jihohi da dama kan ce suna da ‘yan gudun hijira kuma abin ba haka bane.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG