Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Yayi Gunduwa Gunduwa Da Abokin Aikinsa


Wani matashi mai aikin gadi mai shekaru ashirin da takwas, mai suna Haruna Abubakar,ya kashe abokin aikinsa, a unguwar Lekki dake jihar Legas.

Rudunar ‘yan Sandan jihar ta Legas ne suka damke Haruna Abubakar, bayan da dan uwan mamacin ya kai koken cewa dan uwansa ya bace tunda yaje aiki bai dawo ba.

A wani bincike da jaridar Vanguard ta gudanar yana nuni da cewa mamacin da wanda ake zargi suna aiki ne a wani gidan gona inda Haruna Abubakar ke zaman mai gadi shi kuwa mamamci wanda ba’a ambaci sunan sa ba yake kiwo..

Da take tabbatar da afkuwar lamarin kakakin ‘yan Sandan jihar ta Legas SP Dolapo Badmos, ta ce Abubakar, wanda ake zargi da mamaci sun sami wata ‘yar takaddama ne daga bisa sai ya rikide ya zama fada inda Haruna Abubakar, da dagin gatari ya kashe mamacin da kuma yin gunduwa gunduwa dashi ya kuma sa shi a cikin wani buhu a jefar a daji.

Hukumar ‘yan Sanda ta ce da zarar an kammala bincike za’a gurfanar da Haruna Abubakar, a gaban kuliya.

XS
SM
MD
LG