'Yan Wasan Kwallo Na Kasar Brazil 76 Suka Hallaka A Hatsarin Jirgin Sama

Akalla mutane 76 sun mutu bayan da wani jirgin sama dauke da ‘yan kwallon kafar wata kungiya daga kasar Brazill ya fado a daren jiya litinin a wajen birnin Medellin (MEDEYIN) na kasar Colombia.

Kwamandan ‘Yan sandan Colomobia, brigadier Janar Jose Gerado Acevedo ya ce biyar daga cikin mutane 81 dake wannan jirgin da aka yi shatarsa, sun kubuta da rai.

Wannan jirgi, mallakar wani karamin kamfanin safarar jiragen saman Venezuela mai suna Lamia, ya taso ne daga Bolivia dauke da wadannan ‘yan wasa da zasu yi wata karawar gasar cin kofin Kwallon kafa na Kasashen Kudancin Amurka a lokacin da ya fado.

Kokarin aikin ceto na fuskantar cikas saboda wahalar zuwa inda hatsarin ya faru, da kuma hazon dake hana ganin nesa.

Shugaban kasar brazil Michael Temer ya ce hukumomi na kokarinb taimakawa kungiyar da iyalan wadanda abin ya shafa. Temer ya ce gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta wajen jajantawa iyalan ‘yan wansan da kuma ‘yan jariodun da suka rasa rayukansu a wannan hatsarin.

Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama na kasar Colombia, Alfredo Bocanegra, ya ce hukumomi suna kokarin tantance ko mai ya kare ma jirgin a sama kafin ya fado, amma kuma a yanzu sun fi mayarda hankali ne ga binciken lalacewar wayoyin lantarki na jirgin.