Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bude Makaranta Karkashin Jami'a Domin Kwas Kan Harkokin Fina Finai - Nasiru Gwangwazo


Nasiru Gwangwazo
Nasiru Gwangwazo

Nasiru gwangwazo shugaban marubata na kannywood, ya ce babban kalubalen da suke fuskanta bai wuce yadda ake kin biyan marabuta hakkinsu ba da zarar sun kammala rubutawa mutum labarinsa.

Ya bayyana hakan ne a yayin da suke tattaunawa da wakiliyar dandalinVOA a wata zantawa da suka da ita.

Marubucin ya bayyana cewa mafi akasari sukan yi gyara ne a rubutun fim kafin a fitar da fim ko bayan an fitar da shi, kuma da zarar sun ga wani gyara, ya ce mafi akasari ayyukan kungiyarsa dai bai wuce kwato wa ‘yan kungiya hakkinsu ba ko.

Babbar nasarar da suka samu a cewar sa itace ta bude wata makaranta karkashin jami’a da za’a rika kwas akan harkar fina-finai wadda wannan wani babban cigaba ne a harkar fina-finai.

A fanninmu na tsegumi kuwa muna da labarai da dumiduminsu inda marubucin ya ce ya shirya wani fim da ba’a taba ganin irinsa ba mai nisan kiwo, ko me ya bambamtashi da labaran da muka saba gani?.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:15 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG