Jami’an ‘yan sanda a jihar Legas sun yi nasarar cafke wasu yaran mota su biyu da aka bayyana na farko mai suna Lateef Sodiq, mai shekaru 22, da haihuwa, da kuma Tunde Lawal mai shekaru 21, da haihuwa bayan sun kwacewa wani mutum motarsa mai kirar Honda Saloon.
Matasan sun bayyana cewa suna cikin kungiyar masu yiwa jama’a fashin motoci a jihar Legas, sun kuma kara da cewa suna rike kawunansu ne tare da taimakon fashin da suke yi.
Sodiq ya bayyanawa mujallar Punch cewar jami’an wadanda suke ta bibiyarsa ba tare da saninsa ba sun kama shi ne yana cikin aikinsa na yaron mota. Ya kara da cewa ranar laraba da yamma bayan ya kammala aikinsa na ranar ne ya je wurin sauran abokan da suke kwacen motoci tare, inda suka kwace motar mai Kirar Honda a yankin Sabo, dake Yaba, suka kuma jefar da direban motar a hanyar Ikorodu.
Sodiq ya kara da cewa basu taba lafiyar direban ba, abinda suka yi kawai shine, tambayarsa lambobin sirrin motar kadai.
Ya bayyana cewa wannan shine karo na biyu da ya bi sauran abokan nasa wajen kwacen motocin jama’a, kuma sun bashi kudi naira dubu hamsain a fitarsu ta farko, ya ce sunan jagoransu Coded, kuma ba’a kama shi ba tunda ya ranta a nakare.
Matashin ya kara da cewa bait aba yin fashi ba, wannan ne watansa na farko cikin wata guda daya isa jihar Legas daga jihar Kwara, sakamakon rashin iya jurewa sana’ar noma da mahaifinsa ya tursasa masa yi wadda bazata iya daukar dawainiyarsa a makaranta ba.
Lawal, kuma cewa yayi hangen fashi da makami a matsayin hanyar samun kudi cikin sauki fiye da yaron mota, ya kara da cewa aikin yaron mota yana wahala kwarai dalilin da yasa ya jefa kansa ciki Kenan, amma a cewar sa, yanzu ya fahimta cewar fashi da makami masifaffiyar sana’a ce. Lawal ya kara da cewa Sodiq ne ya jawo cikin wannan muguwar sana’a.
Kwamishinan ‘yansandan ya bayyana cewa suna ci gaba do kakarin ganin sun sami nasarar cafke sauran abokan fashin.