Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Gaggauta Binciken Dattijon Da Ya Yi Wa 'Ya Ta Fyade- Inji Hadiza Abubabar


Hadiza Abubabar, mahaifiyar wata yarinya mai shekaru 9 da haihuwa ta ce wani dattijo makwabcinsu ne yayi wa ‘yarta fyade tun bayan babbar sallah har kawo yanzu ba’a hukunta shi ba.

Ta kara da cewa dattijon dai ya yiwa diyar tata fyade ne a unguwar Hototon Walawai a jihar Kanon Nijeriya

Mahaifiyar yarinyar ta ce tun bayan da aka yi wa di‘yar ta ta fyaden bayan babban sallah, har kawo yanzu ba’a hukunta mai laifin ba, gashi kuma yarinyar na fama da wani ciwo da ya fito mata a matancinta wanda ya ke hanasu bacci da zarar dare yayi .

Ta ce wani nama ne ya fito a matancin yariyar, inda take bukatar mahukunta da su taimaka wajen gaggauta bincike domin a kwato musu hakkinsu, tare da hukunta mai laifin.

Domin jin gaskiyar alma’arin mun tuntubi Kakakin babban kotun jihar Kano Baba Jibo Ibrahim wanda ya tabbatar da cewa tabas da akwai karar a kotun , tare da ba ta hakuri, da ta saurara har sai an yi bincike akan lamarin.

Ga cikakken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG