Kimanin dubun-dubatan matasa ne a baki daya Najeriya, ke fuskantar tirjiya wajen samun guraben karatu, a jami’o’i da kwalejojin ilimi da kimiyya. Bisa dalilin rashin samun wadatattun maki wajen jarabawar share fage ta JAMB.
Hukumar na kokarin kawo karshen wannan matsalar, inda shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyanar da irin matakan da suke dauka, don kawo karshen wahalar. Duk dai da cewar hukumar na daukan matakai da suka kamata wajen fitowa da adadin makin, da ake warewa a kowace shekara, ya bayyanar da cewar, sukan hadu da hukumomi da duk suke karkashin ma’aikatar ilimi, don fitowa da adadin makin a kowace shekara.
Yanzu haka suna kokarin gyara duk hanyoyi da suka kamata, a dauka wajen inganta jarabawar, da kuma kokarin bama matasa damar samun gurabe a wasu makarantu, da basu samu damar cike guraben suba, suna kokarin tsayar da maki 180, a matsayin maki da kowane dalibi ya kamata ya samu kamin a karbe shi a makarantun.
Hukumar zasu kokarta wajen bama jami'o'in shawarwari dangane da makin dalibai, don basu da bukatar ganin yadda jami'o'i ke korar yara, batare da basu damar da zasu bayyanar da irin basirar da Allah ya basu ba. Yunkurin su shine su zama tsakanin dalibai da jami'o'i.
Amma idan mutun yana da maki da yake kusa da 180, kuma makaranta basu samu dalibai da suka cike gurbin suba, to zasu bama sauran dalibai damar shiga koda kuwa suna da karanci maki. Ya kuma kara da cewar yanzu haka suna iya bakin kokarin su, wajen ganin sun kawo karshen karancin guraben karatu.
Haka suna kokari wajen saukaka komai, don haka yasa suka kara damar cika fom da canza duk wani bayanai da mutun ke bukata ta yanar gizo, yanzu haka babu bukatar mutun yaje ofishin su, duk abun da mutun ke bukata zai iya samun shi a shafin su kai tsaye.