An danganta kishi tsakanin matan aure akan maigidan, wasu mata da suka yi mahawara akan batun kishi a zauren mu na yau da gobe, sunce tun ranar gini ranar zane.
Daya daga cikin matan da suka tattauna Hajiya Kande Buba, tace kishiya har abada kishiya ce, ta kara da cewa a wasu lokuta akan samu kishiyoyi suna zaune lafiya,wannan ya danganta ga miji,
Ta kara da cewa tun daga ranar da miji ya fita neman aure ya kyautu ya fara sanin abinda zai fito bakinsa domin sau lokuta da dama sukan kwashe labarin gida su gayawa Amaryar tun ma kafin ta shigo.
Ita kuwa Hajiya Gude Suleiman, cewa tayi akwai kyakkyawan kishi akwai mummunar kishi acewarta inda yake akwai kyakkyawar kishi shi kansa mai gidan taka tsan tsan zai yi domin ya tabbatar da cewa duk wace ya tabo tafkar ya tabo sauran ne, inda mummunar ko dadin fade ma babu domin abin babu dadi.
Hajiya Salamatu N’djamena, ita kuwa cewa tayi daya daga cikin abubuwan da ke jawo rashin jituwa tsakanin kishiyoyi, shine kananan maganganu wasu lokuta daga bakin maigida, domin wasu mazaje basu so ganin kan matansu a hade domin ya kan dama masu lissafi.