Farfesa Ya Cika Alkawalin Lamushe Kwari Idan Trump Ya Lashe Zabe!

Farfesa Sam Wang

Kyan alkawali cikawa! Farfesa Sam Wang, shahararren malami ne, kuma masani ne a harkar zabe, a jami’ar “Princeton” dake kasar Amurka, a ‘yan kwankin baya ne dai ya bayyanar da cewar, dan takarar shugabancin kasar Amurka karkashin jam’iyar “Republican Party” ba zai ci zaben ba.

Ya kara da cewar idan kuwa har Mr. Donald Trump, yaci zaben, koma ya samu lashe kujerar wakilai 240, to babu shakka zai ci kwari. Domin alkalunma sun bayyanar da tabbacin cewar ‘yar takara Hillary Clinton, zata lashe zaben. Bisa dalilin bincike da ya gudanar da ya bayyanar da ra’ayin jama’a suna tare da ita.

Tun a ranar 19, ga watan Oktoba, ne Farfesa Wang, ya rubuta a shafin shi na tweeter kan cewar idan Trump yaci zabe, zai ci kwari. Hakan yasa ya cika alkawalin shi, a wata tattaunawa da su kayi da ma’aikacin CNN Mr. Michael Smerconish. Biyo bayan sakamakon zabe inda zababben shugaba Trump ya samu kujeru 290, ita kuwa Hillary ta samu 228.

Rahotannin dai sun bayyanar da cewar, a wannan karon binciken da masana harkar siyasa suka gabatar yayi karya, domin kuwa babu wani wanda bai yi tsammanin cewar uwargida Hillary, ce zata lashe zaben ba, amma sai ga akasin hakan. Hakan ya sa mutane da dama shiga cikin rudanin zabe, haka mutane da dama sunyi alhinin yadda zaben ya kasance.