Wakar Soyayya Bata Cikin Al'adar Hausa Kamar Yadda Ake Nunawa A Fina Finai - Inji Kasimu Yero

Kasimu Yero

A ci gaba da hirarmu da fitattacen jarumin nan da ya ga jiya, ya ga yau a fagen wasannin kwaikwayo tun a wancan karni wato Kasimu Yero, a wannan karon ya cigaba da bayyana bambancin Kalmar nan ta soyayya da kauna.

Ya ce soyayya bata daga cikin al’adun malam bahaushe kamar yadda ake nuna wa a fina-finai illa kauna, inda ya kara da cewa lokaci yayi da yakamata a fara nuna wasu matsaloli da suke damun alumma ta hanyar fina finai.

A fannin tsegumi kuwa, mawakin nan 2face Idibia, a wata tattaunawa da manema labarai ya bayyana cewa ya so a ce yaransa bakwai sun zo daga uwa guda , mawakin dai ya fara waka ne a lokacin suna hadaka da kungiyar Plantashun boiz, kafin daga bisani kowannensu ya kama gabansa 2face dai na da yara bakwai a yanzu.

Saurari cikakken rahoton a nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Wakar Soyayya Bata Cikin Al'adar Hausa Kamar Yadda Ake Nunawa A Fina Finai - Inji Kasimu Yero