Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta cafke wani matashi mai shekaru talatin da biyar wanda ya shahara wajen karbar kudi a hannu mata da barazanar cewa ko zu bashi kudi ko kuma ya wallafa hotunan tsaraicinsu a yanar gizo.
Matashi mai suna Atanda Michael, wanda ya karanci kwamfuta, bangaren rundunar ‘yan Sandan jihar na gaggawa ne ta cafke baya da akayi kwanaki ana biye dashi.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan Sandan ta fitar ta ce wanda ake zargin tsohon mai laifi ne wanda aka taba kullewa wanda yanzu haka yana da shara’a a kotu akan makamanci abinda ya aikata inda ya karbi Naira dubu dari bakwai daga hannun wata mata da suka sadu ta hanyar wani dandali wa zawartaka.
Wadanda ya karbi Kudaden daga hannunsu na baya bayan nan sune Funmilola, 10,000, Motunrayo 6,000, Joy, 5,000, da Lizzy, 100,000.
Lizzy, ce ta kai kara ga hukumar ‘yan Sandan in ji kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar SP Dolapo Badmus, a lokacin da yake tabbatr da afkuwar lamarin.