A farkon shekarar nan ne aka kama wasu dalibai yan kasar Thai, masu zana jarabawar shiga wata babbar makarantar koyon aikin likita. An kama su ne suna suna kallon takardun jarabawar su, da wannan gilashi na ido wanda wannan gilashin yake aikawa abokanan su, da ke waje sako su kuma suna aiko musu da ansar ta agogon hannu.
Wannan babban kalubale ne, ganin wadannan daliban masu niyyar koyon aikin jinya ne. Manyan na’urorin da dalibai ke amfani dasu, wajen satar ansa shine karar wayar sadarwar su, wanda yara ne kawai suke ji manya basu ji, wanda idan ka kai shekara 30 ko 35 ba zaka ji karar wayar ba. Saboda haka da shi suke amfani sai su kadai suke jin ansoshin da ake basu a kunnunwan su.
Satar ansa a jarabwa babban kalubale ne, a harkar ilimi a cewar Mr. Denise Pope, wani babban malami a jami’ar Stanford yace daliban da ke satar ansa, yawanci su masu kokari ne suna dai satar ansar ne saboda suna son su samu maki mai yawa, ko kuma aiki yayi yawa suna son su samu saukin aikin makaranta.
Yace babbar hanyar da za’a bi a magance wannan matsala shine, malamai su canza yanda suke koyar da dalibai, a zauna da dalibai da malami a tattauna yanda za’a shawo matsalar, sannan a jaddada ma dalibai mahimmacin gaskiya a al’amuran su.